Disneyland 1972 Love the old s
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Tambayoyi da amsarsu tare da Mallam Ibrahim Zakzaky na ashirin da uku

Sayyed Zakzaky2

Hukuncin mai adashin da ke ajiya a banki

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Mutum ne ana bin sa bashin salloli masu yawa, shin zai iya yin sallar tahajjud ko kuma nafila kowace iri?

SHAIKH ZAKZAKY: Eh haka ne, idan mutum ana bin sa bashin sallar farali yana iya yin nafila, wannan haka yake dangane da salla. Na san mun sha amsa wannan. Cewa azumi ne, ba a yarda ana bin ka bashin azumi ka yi nafila ba, ko ka yi kuma bai inganta ba.


TAMBAYA: Akramakallah. Shin ya halasta sayar da maganin bera?

Daga Saleh Shehu Yadin Lere, jihar Kaduna.

SHAIKH ZAKZAKY: Lallai ba laifi ga sayar da maganin bera saboda kashe bera ba laifi ne ba. Sai dai in abin da ake amfani da shi wajen kashe shi din, kamar abin da zai ci ne ya mutu ko ya gudu ko abin da ya yi kama da haka nan, amma ban da konawa da wuta. Kona abu da wuta ne bai halasta ba. Don riwayar cewa babu mai azaba da wuta sai Ubangijin wuta. Saboda haka kashe bera ya halasta da dukkan kwari masu cutarwa. Amma idan ya san wanda zai saidawa, zai yi amfani da shi ba ta wannan ba, ta wata hanya daban da ba ta halasta ba, to ba zai sai da masa ba.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Mutum ne ya dade yana neman auren wata yarinya, sai daga baya ta lalace, har sunanta ya bayyana da sunan fasikanci, shin ya hakura a daura masa aure da ita, ko kuwa ya je ya samu wata ya aura?

Daga Yusuf Usman Kaura Namoda.

SHAIKH ZAKZAKY: Bai halatta ba ya auri fasika wadda har sunanta ya shahara da haka nan. Kuma wajibinsa ne ma in zai yi aure din ya ga ya auri mutumiyar kirki ne, don ya kiyaye gidansa kuma ya kyautata uwar 'ya'yansa. A takaice bai halatta ba auren fasika.

TAMBAYA: Akramakallah. Mutum ne tafiya ta kama shi, kuma ta isa kasaru, amma bai sani ba zai kai kwana 10 ko ba zai kai ba, shin kasaru zai yi ko cikawa?

SHAIKH ZAKZAKY: Lalle kasaru zai ta yi sai har ya yanke shawarar zai kwana 10. Ko da ma mukaddara lokacin da ya je yana zauna yana tunanin ya tashi yau, ya tashi gobe, to yana ta yin kasaru. To sai lokacin da ya zartar da shawarar zai kwana 10, zai fara daga lokacin da ya natsu da shawarar, ba daga lokacin da ya isa garin ba. Wato mu kaddara kenan ko da abin ya kwana 10 ne yana kasru, to sai kuma ya zartar da shawarar zai sake wasu kwana 10, to shi kenan daga lokacin zai fara cika salla kenan. Amma ana cewa idan ya yi, yana ya tashi yau, ya tashi gobe, in ya yi wata daya a kan wannan hali, to dole sai ya cika salla.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Mutum ne yake aiki a wani gari, amma yana tafiya ne ranar Litinin ya dawo ranar Juma'a, wani lokaci kuma ya yi sawu biyu a sati. Wani Malami ya ce da shi shi mai gari biyu ne saboda haka cikawa zai yi. Wani kuma ya ce masa kasaru zai yi, meye gaskiyar maganar?

SHAIKH ZAKZAKY: Ana gane mai gari biyu ne in yana da gida a can. In yana da gida a can, misali da iyali, to ya zama mai gari biyu. Amma in dai zuwa kawai yake yin Bizines dinsa ya dawo bai da gida, to lallai bai zama mai gari biyu ba. Sai in yana da gida. Ko ba iyali, amma yana da gida yana zaune a wurin, to shi ne zai zama mai gari biyu. In kana zuwa gari a matsayin bako, ba ka da gida, ba ka zama mai garin ba, ba ka zama mazaunin garin ba, sai ranar da ka sami gidan zama, ya zama nan kake sauka da'iman. Allahumma ko da kuwa haya ka yi, ya zama gidanka.

Saboda haka idan mutum mai gari biyu ne, cika salla zai yi a kowane gari, ya zama shi ko'ina ya je gida kenan. To idan kuwa mai gari daya ne, to a inda ya tafi ya zama matafiyi. Ma'ana abin da muke nufi da mai gari biyu shi ne, in ya je wannan garin shi ya tashi a matafiyi.

TAMBAYA: Akramakallah. Wani ya taba ce min in mutum ya makara a kan yin azumin nafila bai yi sahur ba, to zai iya cin abincinsa da safe ya wuce da azumi, kuma azumin ya yi. Shin haka ne ?

Daga Garba Musa Malam Madori, jihar Jigawa.

SHAIKH ZAKZAKY: Lalle ba haka bane. Wanda ya gaya masa haka nan ya dai fada masa ne da ka, amma ba wata hujja. Abin da aka sani shi ne, azumi ana yin sa ne tsakanin ketowar alfijir da faduwar rana, faduwar rana na hakika. Kuma ba yadda za a yi bayan ketowar alfijir mutum da gangan ya ci abinci kuma ya ce yana azumi.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam mutum ne ya yi zina da wata mata. Bayan ya gane kurensa ya tuba, ko zai iya auren diyarta?

Daga wani da bai sa suna ba

SHAIKH ZAKZAKY: To har abada ba zai iya yiwuwa ya auri diyarta ba. Amma in ita

kanta matar ne, ana iya cewa eh, in ba ta yi ciki da shi ba. In ta yi ciki ta haihu da shi,

to shi ma har abada ba zai aure ta ba.

TAMBAYA: Akramakallah, nine na sayi wake a lokacin da yake araha na ajiye a matsayin in na tashi neman kudi zan sayar. To amma ban tashi sayarwa ba sai da na ga ya yi tsada. Shin ya matsayin haka a addini?

Daga A. A. Kaduna

SHAIKH ZAKZAKY: Eh, babu laifi matukar bai shiga cikin ma'anar Ihtikar ba. Abin da ake ce ma ma'anar Ihtikar shi ne boye kayan abinci alhali akwai masu bukata domin sai ya yi tsada a fito da shi a sayar. Amma idan bai kawo karanci ba a kasuwa, ya zama ta yadda babu shi, amma shi ko ya boye shi ba, to babu komai.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, ya halatta mutumin da yake sayar da kayan abinci irin su masara, wake da sauransu ya saya da yawa ya ajiye yana sayarwa kadan-kadan? Idan mutum yana sayarwa sai kayan suka tashi a kasuwa zai iya kara kudin nasa kayan shi ma kamar yadda yake a kasuwa, duk da cewa ba yanzu ya sayi kayan ba?

Daga Sama'ila Turaki Kakuri Kaduna.

SHAIKH ZAKZAKY: To kamar tambaya ta baya ne muna iya cewa eh haka ne ya halasta matukar bai je ga matsayin Ihtikar ba . Kuma Ihtikar shi ne mutun ya boye abinci a rasa alhali ga mabukatansa yana bidan in ya yi tsada ya sayar. To in bai kai ga wannan haddi ba ya halasta, in kuma ya kai haddin Ihtikari, to ya haramta. Ba lale ne in zai sayar ya yi la'akari da yadda ya saya ba, zai sayar ne a kudinsa na kasuwa.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam mutum ne ya tambaye ni kudi, saboda nauyinsa da nake ji sai na ba shi. Da akwai lada ko ba lada?

Daga Danladi 'yar Dutse 08054481107

SHAIKH ZAKZAKY: To da lada tunda dai har ka ji nauyinsa ka ba shi. Allahumma ko da ma ya tilasta ka ne ma ka ba shi, duk da haka dai za ka sami lada kai. Sai da shi in ya kuntata maka shi ne ya yi laifi. Ya san cewa in ya tambaye ka kai za ka ji nauyi ka ba shi kuma za ka shiga takura, to shi abin da ya yi bai dace ba. Amma kai kam ba za ka rasa ladanka ba.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam. Ina jinin haila, sai janaba ta same ni. Idan jinin ya tsaya zan yi wankan janaba ne, sannan na yi na haila, ko kuwa idan na yi daya ya wadatar da su?

Daga Hannatu Muhammad Kaduna

SHAIKH ZAKZAKY: Abin sani shi ne, tana iya yiwuwa mace tana cikin janaba ba ta yi wanka ba sai haila ta zo, wanda kuma duk wanka biyun ne zai hau kanta. Na haila wajibinta ne ta yi wanka in ya dauke, in hailar ta kare ne za ta yi wanka. Shi ana yin sa ne sakamakon karewar jinin haila din. Ita kuwa janaba, da zarar ya hau ta da ma lazim ne ta yi wanka. Saboda haka wankokin nan daya bai kau da daya ba. Allahumma sai dai in ta yi jinkiri ne, mukaddara, ta yi jinkiri ne da janaba har lokacin karewar haila din, to tana iya yin wanka daya da niyya biyu.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam, a wannan zamani namu, mata sukan yi wasu abubuwa kamar maza, duk da cewa akwai matakai masu tsauri, amma sai na ga abubuwa ne masu wuyar ganewa idan aka duba wadancan dokokin. Abubuwan kuwa sune:

Faretin mata. A taron Musulunci na duniya a kan sa mace ita ce shugabar taron, duk da cewa akwai haramcin maganar mace a cikin maza, in ba da larura ba. Wani lokacin a wajen taro akan sa mace ita ce ke gabatar da mai jawabi idan wurin taron mata ne.

Abun da ya shafi koyar da karatu ga mata, sukan je wasu mazan suna koyar musu wadanda ba mazajensu ba, wanda mutane da yawa suna ganin bai dace ba.

A matsayina na mai tajdidi, me zan gayawa wanda bai fahimci abin ba?

Daga Adamu Muhammad Azare jihar Bauci (adammazare@yahoo.com)

SHAIKH ZAKZAKY: Na farko dai, mace ta yi kama da maza a shiga, shi ne aka nuna haramcinsa. Amma shi wadannan abubuwan da ya lissafta lalle ba su kebanta da maza ba, ba su a cikin abubuwan da ake ganin khususiyyan maza ne koma bayan mata ba. Sai dai kamar yadda yake cewa su mutane suna ganin bai dace din bane kawai, ba wai domin shiri'a ce ta ce bai dace ba.

TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam ni dai mai adashi ne, tun lokacin da na fara nake kai kudi banki kuma sukan kara min kudin ruwa a kai, kuma an ce haramun ne cin su, to Malam ina fatan za a warware min kaina don na san yadda zan yi da kudin.

Daga Musa Yau Fagge d2 Jihar Kano (yaumusa@yahoo.com)

SHAIKH ZAKZAKY: A nan an gwama abubuwa biyu, adashi da ajiya a banki. Na san a baya mun sha amsa tambaya dangane da ajiyar banki da kuma yadda mutum zai yi da ruwa din in an kara masa. Muka ce idan bankin na Musulmi ne, to da ma tun farko kamata ya yi ya zama a wani irin salo ne na raba riba da hasara. Amma idan bankin ba na musulmi bane, to dama lallai, babu damuwa zai iya karbar abinsa kuma ya halasta masa. Saboda haka tunda nan ta gwama shi tare da adashi, to sai mu ce idan aka yi ajiya din a bankin da yake ba na musulmi ba, to shi abin da ya karu a kai din shi ma za ta kara wa masu adashin ne don nasu ne. Amma in muka kaddara shi musulmi yana bayarwa, to zai zama kenan shi ruwan ba zai halatta ta yi amfani da shi ga kanta ko ga wani abin da zai amfane ta ba. Amma tana iya kai shi ga wani wurin da al'umma za ta amfana da shi, kamar masallaci koabin da ya yi kama da haka nan. Ko kuma ta wata fuska idan ya cakudu, ta fitar da Khumusi.

TAMBAYA: Mace ce aka sake ta tana jinin haila, shin wannan sakin yana nan ko ba ya nan ?

Daga Daga Ibrahim Imam 0802 7394023

SHAIKH ZAKZAKY: Dama cikin sharadin saki, ba a yin sa sai ya cika sharudda. Daga ciki akwai cewa dole ya zama ta yi tsarki kuma ba a take ta ba. Shi ne ma'anar, Fa dallikuhunna li iddatihinna. Wato ku sake su a yayin lokacin sakinsu. Sannan kuma ya zama sakin nan ya yi insha'insa ne ga shaidu adilai biyu alal akalla. Idan ya saki mace, tana haila, tunda ya saba ka'ida, to bai zama saki ba. Wannan a ra'ayi sahihi. Amma akwai masu cewa ana tilasta masa komawa da ita ne, amma suna karbar sakin. Amma sahihin magana shi ne bai ma yi bane. Tunda in aka yi abu ya saba ka'ida, ba kuma za a karbe shi ba.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din